19-Jun-2025
18-Jun-2025
17-Jun-2025
20250619-Yamai
00:00
1x
A cikin ’yan shekarun baya bayan nan, bisa jagorancin tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping kan kiyaye muhalli, kasar Sin ba kawai ta karfafa kiyaye muhallinta ba, har ma tana dagewa wajen ingiza manufar al’umma mai makoma bai daya ta daukacin bil ’adama, da shiga cikin ayyukan kula da muhalli na duniya, da yin aiki tare da dukkan bangarori wajen sa kaimi ga gina duniya mai tsafta, kyakkyawa da ci gaba mai dorewa ta hanyar daukar matakai na zahiri. A cikin shirinmu na yau, zan gabatar muku yadda kasar Sin da kasashen Afirka ke inganta ci gaba ta hanyar hadin gwiwa a fannin kiyaye muhalli.
Kasuwancin Sin da Afirka ya kai wuri-na-guguna-wuri har dalar Amurka biliyan 295.56 a shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 4.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara kuma wani abun burgewa, ya kasance yana samun bunkasa a tsawon shekaru 16 a jere, inda hakan ya kara tabbatar da kasar Sin a matsayin babbar abokiyar kasuwancin naihyar Afirka. A halin yanzu, bisa goyon bayan wasu muhimman tsare-tsaren ayyukan hadin gwiwa guda 10, 'yan kasuwan Sin da na Afirka suna kara yin hadin gwiwa a dukkan sassan masana'antu, da sa kaimi ga kyautata dangantakar dake tsakaninsu, da samar da wani sabon ci gaba a fannin bunkasa tattalin arziki mai dorewa.
A yankin tudu mai tsayin mita 4000 mai yanayin sanyin kasa da maki 20 na sentigred, membobin kungiyar mata masu binciken kayan tarihi suna amfani da sandan gora, da karamin shebur wajen kawar da duwatsu da kura, don binciken kayan tarihi dake shaida mu’amalar kabilu daban daban na kasar Sin a cikin shekaru fiye da dubu daya da suka gabata.
20-Jun-2025
27-May-2025
13-Jun-2025